1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jimamin kisan nukiliya na Hiroshima

August 6, 2023

Albarkacin bikin tunawa da bam din nukiliya na Hiroshima, mahukunta a Japan sun yi kira ga shugabannin duniya su guje wa amfani da makamin nukiliya a wannan zamani.

https://p.dw.com/p/4UpgI
Hoto: Keita Iijima/Yomiuri Shimbun/AP/picture alliance

Japan na bikin tunawa da mummunan harin nukiliya na farko da aka kaddamar a kanta shekaru 78 da suka wuce a lokacin yakin duniya na biyu. Kararrawa da ke alamta zaman lafiya ta kada a daidai karfe 8:15am ( na safe agogon Japan) na wannan Lahadi, daidai da lokacin ranar 6 ga watan Agusta na 1945 da Amurka ta jefa bam na nukiliya a kan mutanen yankin na Hiroshima da ya halaka mutum kimanin 140,000.

Albarkacin bikin na bana wanda ya tara mutane wajen 50,000 cikinsu har da tsofaffi wadanda suka tsallake rijiya da baya a wannan hari na nukiliya, magajin garin Hiroshima Kazumi Matsui, ya yi kira ga kasashen duniya da su kauce wa amfani da makamin nukiliya a wannan zamani. Hakan dai na zuwa ne a yayin da manyan kasashe musamman kasar Rasha ke barazanar amfani da shi a yakin da take yi da Ukraine.