Holland: Hukunci kan safarar makamai
April 22, 2017Talla
Kotun wadda ta yanke masa daurin shekaru 19 na dauri, ta ce ta gano mutumin da ke dillancin katako, ya yi wasu kamfanoni biyu a kasar Liberia a farkon shekarun 2000, ya kuma yi amfani da kamfanonin nasa wajen safarar makamai zuwa kasar ta Liberia. Kotun dai ta yanke masa hukunci ne saboda laifin taimaka wa yaki, da kuma ke zama laifi irin na yakin.