Haramta burqa da nikabi a Holland
August 1, 2019Talla
Daga cikin wuraren da dokar za tayi aika sun hada da gine-ginen gwamnati da asibitoci da makarantu da motoci da jiragen haya da ke jigila a sassan kasar.
Tuni dai kungiyoyin Musulmi da na kare hakkin dan Adam a kasar suka nuna rashin amincewarsu da dokar yayin da wata jam'iya da ke da alaka da addinin Islama a birnin Rotterdam ta ce za ta biya tarar Euro 150 da za a karba ga duk wanda hukuma ta kama da karya dokar.
Wani dan majalisa mai suna Geert Wilders da ya yi fice wajen sukar addinin Islama a kasar ne ya fara tado da maganar haramta amfani da Burka a kasar shekaru 10 da suka gabata kafin daga bisani majalisar dokokin kasar ta amince da batun a shekarar da ta gabata.