1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hong Kong: Hari kan masu zanga-zanga

Abdoulaye Mamane Amadou
July 21, 2019

Wasu mutanen da kawo yanzu ba a tantance su ba sun kai farmaki a yau Lahadi kan masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a yankin Hong Kong, daidai lokacin da 'yan sanda ke kokarin tarwatsa masu zanga-zangar.

https://p.dw.com/p/3MTP4
Anti-Auslieferungsproteste in Hongkong
Hoto: Getty Images/Billy H.C. Kwok

Kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewa ko a gundumar Yuen Long dab da iyakar yankin da kasar China a arewa maso gabashin Hong Kong, wasu mautane da suka rufe fukokinsu sun kai hari ga masu zanga-zanga, tare da jikkata wani dan jaridar mai aikewa jaridar Stand News labarai.

A yau din nan ne dai wata sabuwar zanga-zanga ta sake barkewa a yankin na Hong Kong, a ci gaba da nuna adawa kan wani kudurin dokar hukunta masu laifin yankin a kasar China.