Hong Kong: Ruwan sama mafi karfi cikin shekaru 140
September 8, 2023Gargadin na kasancewa na farko tun bayan wanda aka yi a watan Octobar shekarar 2021. Birnin na kasar China ya fuskanci saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya da ba a taba gani ba cikin shekaru 140.
Masana na cewa, mahaukaciyar guguwar nan ta Haikui ta haifar da saukar ruwan sama mai karfi a lardin Guangdong da ke iyaka da birnin na Hong Kong.
Karin bayani: Guguwar Haikui na barazana a Taiwan
A yanzu haka dai, gwamnati ta sanar da rufe makarantu sakamakon barnar da ambaliyar ruwan ta haifar, kana aka shawarci ma'aikata da su zauna a gida.
Shugaban birnin na Hong Kong, John Lee ya nuna alhininsa game da iftila'in ya na mai bada umurni ga dukannin masu ruwa da tsaki da su dauki matakin gaggawa.
Ko a makon da ya gabata, Kudancin kasar ta China ya fuskanci mahaukaciyar guguwar nan ta Saola.