Dakon masu zanga-zanga a Hong Kong
May 27, 2020Talla
Wasu tarin 'yan sandan kwantar da tarzoma a cikin shirin ko takwana sun harba hayaki mai sa kwalla kan masu zanga-zanga a harabar majalisar dokokin yankin Hong Kong, a wani yukuri na dakile zanga-zangar da ka da ta barke gabanin wata muhawarar da majalisar ke shirin yi a yau kan wannan sabon kudrin dokar. Shedun gani da ido sun ce an jibge dubban 'yan sandar kwantar da tarzoma inda suka ja daga a dab da harabar majalisar, a daidai lokacin da ake sa ran tabka muhawarar tare da jefa kuri'ar na'am kan wani sabon kudrin dokar a game da sha'anin tabbatar da tsaro.