Yunkurin masu neman sauyi a Hong Kong
August 12, 2019Talla
Masu boren da ke sanye da bakaken tufafi na yin wani gangami ne na fadikar da baki da ke shigowa bukatarsu na ganin an girka tsarin dimukaradiyya a yankin da ke a karkashin ikon China. Gwamnatin China uwargijiyar ta Hong Kong ta ce yunkurin na masu zanga- zangar da suka soma tun a cikin watan Yunin da ya gabata domin neman yancin gishin kai, da tsarin dimukaradiyya na kama da ta'addanci.