Tsohon Shugaban Masar Mubarak ya rasu
February 25, 2020Talla
Mubarak ya yi mulkin Masar na tsawon shekaru 30. An hambarar da gwamnatinsa a sakamakon zanga zangar gama gari a shekarar 2011.
Watanni biyu bayan da ya sauka daga karagar mulki aka kama shi inda aka tsare shi a gidan yari da kuma asibitin soji har zuwa shekarar 2017 lokacin da aka sake shi bayan da kotun daukaka kara ta wanke shi daga tuhumar da aka yi masa ta bayar da umarnin kisan masu zanga zanga.
Yan Masar da dama wadanda suka zauna zamanin mulkin Mubarak sun baiyana lokacin a matsayin na kama karya da kuma jari hujja.
Gwamnatin kasar ta Masar ta baiyana zaman makoki na kwanaki uku domin nuna alhini ga mamacin.