1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaron da hoton gawarsa ya girgiza duniya

Mohammad Nasiru Awal/YBSeptember 4, 2015

Tambaya ita ce ko daidai ne a wallafa wannan hoto? Shin dole tashar DW ta wallafa shi? Idan ba dole ba ne menene dalili?

https://p.dw.com/p/1GRNN
EINSCHRÄNKUNG IM TEXT BEACHTEN! Dieses Bild soll nur als Artikelbild zum Kommentar des Chefredakteurs gebucht werden Türkei Bodrum Aylan Kurdi
Hoto: Reuters/Stringer

A ranar Juma'a (04.09.15) aka yi jana'izar yaron nan dan Siriya da ruwa ya ci shi lokacin da shi da iyayensa ke kokarin tsallake teku a Turkiya zuwa Turai. Hoton gawar yaron dan Siriya Aylan Kurdi da aka dauka lokacin da ruwa ya turo shi gabar teku ya kada duniya baki daya. Amma tambaya a nan ita ce shin ko ya kamata a wallafa irin wannan hoto ko ma ya zama dole a wallafi shi? Babban editan tashar DW Alexander Kudascheff ya rubuta sharhi game da sharwar da DW ta yanke a kan wannan tambaya.

Hoton dai mai tada hankali, wanda kuma ya nuna irin wahala da kasadar da ake dauka na tsere wa daga yakin basasar da ya daidaita kasar Siriya. Hoto da aka dauka wanda kuma ke nuna abubuwan da ke wakana kullum a tekun Bahar Rum.

Hoton ya kuma tabbatar da bala'in yakin basasar na Siriya. Hoto ne mai sa kaduwa. Hoto ne kuma da ke sa mutum rasa yin magana saboda bacin rai. Hoto ne da ke kuma bayyana rashin ikonmu. Hoto ne kuma da ke sa mutum cikin tunani mai zurfi. Hoto ne da watakila za a iya cewa na shekara ko ma na shekaru gommai. Ya dai kunshi dukkan abubuwa masu tayar mana da hankali wanda ke sanya mu cikin kaduwa da fushi a cikin watannin bayan nan. Mummunan hoto ne.

Sai dai tambaya ita ce ko daidai ne a wallafa wannan hoto? Shin dole tashar DW ta wallafa shi? Akwai dalilai gamsassu akwai kuma dalilai masu saka ayar tambaya na ka da a wallafa hoton. Wannan dai ya shafi kare mutuncin yaron da hakkinsa da kuma nuna halin ya kamata daga bangaren mu kafafan yada labarai.

Alexander Kudascheff DW Chefredakteur Kommentar Bild
Alexander Kudascheff: Babban edita a DWHoto: DW/M. Müller

Sai dai DW ta yanke shawarar wallafa hoton ba wai don neman burge jama'a ko neman karin masu shiga shafukanta na intanet ko fadada yankunan da shirye-shiryenta na telebijin ke kaiwa ba. Mun nuna hoton ne domin ya kadamu, ya kuma zama alamar bala'in da 'yan gudun hijirar ke fama da shi, musamman ga yaron da bai da laifi, wanda iyayensa suka dauki kasadar yin tafiya mai hadari domin sama masa wata makoma kyakkyawa, amma ta kai ga ajalinsa a teku.

Mun nuna hoton ne domin ya tayar mana da hankali wanda ya samu tunani mai zurfi a lokacin taron editoci na tashar DW. Mun kadu da samun wannan labari na bakin ciki na mutuwar wannan yaro. Muna nuna hoton ne don nuna alhini da yi wa iyalinsa jaje.