Hotuna masu bayani na Akinbode Akinbiyi
Mai sana'ar daukar hotuna 'dan Najeriya, mazaunin Jamus tsahon shekaru 50, da ya kan zagaya kasashen duniya domin daukar hotuna iri-iri a birane da wajen gari. An baje ayyukansa a filin bajekolin hotuna na birnin Berlin
'Mai daukar hoto a tafiye''
Akinbode ya kwatanta kansa da wanda yake yawon ''yin'' maimakon daukar hotuna. A Berlin yake zaune, amma ya kan yi tafiye-tafiye a Afirka, tare da na'urarsa ta daukar hoto, mai saiti zuwa gurare irin su Afirka ta Kudu da Mali, inda aka dauki wannan hoton. Ya samu kyautar sarka na Goethe a 2016, kuma ya fafata a gasar "Documenta 14" a Athens da Kassel a 2017, kuma ya baje fasaharsa a fadin duniya.
Nazari kan birni mai sauyawa
A jerin ayyukansa na ''Sea Never Dry'', Akinbiyi ya bayyana gabar tekun Bar Beach kusa da birnin Legas da ke Najeriya. Wanda a da aka sani da matattarar hada-hadar 'yan gari, tun da ya dauki hotunan a 2016, aka kashe wurin saboda ajiyar kayan gine-gine domin gina birnin Atlantic, mai shigen Dubai ta fuskar ci-gaba. Mai dauke da mutane miliyan 18, ana kallon Legas a matsayin babban birni a yankin.
Nuna yanayin rayuwar mutane a waje
Matan da ke cikin hotunan suna sanye da fararen tufafi don nuna alakarsu da mujami'un Pentecostal. Mutanen mujami'ar da ke wake-wake mai daukar tsawon awanni suna yi, wanda zai iya damun makobta a cewar Akinbiyi, yana wakana ne a bainar jama'a da bakin teku kafin a rufe wurin ga mutane. A ranakun karshen mako masu raye-rayen na bauta sukan kwashe tsawon daren a gabar teku cikin wannan yanayi.
Daukar hoto cikin gaggawa
Daukar hotuna a birnin Legas a inda aka rubuta ''Daukar hoto cikin gaggawa'' akwai wanda yake gurin cikin karamin tenti, yana daukar masu bukatar hotuna kamar na su fasfo, domin amfani da su a ofishin jakadanci da ke kusa da wurin, amma ba su da wadataccen lokacin jira. Aikin Akinbiyi da ya fito a lokacin baje koli, yana nuni ga yadda ake amfani da hotuna ta hanyoyi dabam-dabam.
Fitowa da danshin Afirka a Berlin
Wannan hoton a cikin jerin ''African Quarter'' na nuna wani layi ne a birnin Berlin da aka sawa sunan da ke janyo kace-nace. Asalin sunan layin Petersallee, ya samu ne daga jagoran mulkin mallaka dan Jamus, inda sunan da aka sauya din yanzu Witbooi, sunan dan Afirka ne mai jagorantar yin tawaye ga mulkin mallaka. Akinbiyi ya dade yana daukar hotunan a kan halin rayuwa a wannan yankin tun 1990.
Lura da hotunan da ke bayyana disashewa
Wannan dakin daukar hotunan a unguwar Kreuzberg da ke Berlin na taka rawar bayyana abubuwan sha'awar da ke cikin sana'ar. Akinbiyi ya lura da cewa wannan dakin hotunan a baya 'bandaki' ne, ko gurin shan kwaya. Hotunansa da yawa na nuna lamura ne kamar yadda suke, babu kare-kare ko rage wani abu daga cikin abin da yake zahiri.
Yanayi na 'ba zata'
Bayyana ko wane irin yanayi na daga cikin ayyukan Akinbiyi. Haka kuma daukar hotunan tallace-tallace na sabbin gine-gine a cibiyoyin aikin gini a Berlin, inda wani mutum da ya zo wucewa ya shiga hoton na Akinbiyi kuma ya ba da ma'ana. Ya kara da cewa ''A sanda nake kokarin daukar hoton a wancan gurin sai kawai ga shi ya zo shigewa, wannan shi ne nake kira ''hoton ba zata.''