HRW na zargin sojan Burkina Faso da kisan fararen hula
January 25, 2024A wani rahoton da ta fitar a ranar Alhamis 25.01.2024, Human Rights Watch ta ce tana zargin sojojin Burkina Faso da kisan akalla fararen hula 60 a hare-haren da suke ikirarin sun kai wa mayakan jihadi a wasu sassan kasar.
Karin bayani: An kashe fararen fula a Burkina
Kungiyar ta ce ta yi hira da shaidu da dama kan wannan lamari da ya auku a cikin watan Ogustan shakarar 2023, kana kuma tana ci gaba da gudanar da bincike a kan hotuna da bidiyo da kuma hutunan tauron dan'Adam da ta tattara domin hakikance gaskiya.
A cikin rahoton kungiyar ta ambato mazaunin wani kauye da ake kira Bouro inda ake kyatata zaton an kashe mutane 28 a sakamakon hare-haren, yana cewa gwamnatin kasar na daukar yankinsu a matsayin na 'yan ta'adda, sannan kuma suna tsoron zuwa asibiti idan suka samu raunika sakamakon hare-haren da sojoji ke kai wa ta sama.
Karin bayani: Burkina Faso: Kara wa'adin dokar ta-baci
A baya-bayan dai Burkina Faso na amfani da sabbin dabarun yaki da 'yan ta'adda, inda take farautarsu da jirage marasa matuka sannan kuma a watsa faya-fayan bidiyon a gidan talabijin na kasar don nuna kuzazin da sojoji ke yi.