Hukumar CENI a Chadi ta ɗage ranar zaɓe
September 27, 2010Talla
Hukumar zaɓen ƙasar Chadi ta ɗage zaɓukan shugaban ƙasa,na majalisar dokoki da ƙananan hukumomin zuwa shekarar 2011 sakamakon matsalolin shirye-shirye.
Hukumar zaɓen ta bayyana cewa a saban jaddawalin zaɓen, za a gudanar da zaɓen majalisar dokoki a ranar 20 ga watar Febrairu, na ƙananan hukumomi kuma 27 ga watan Maris kana a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa zagaye na farko a ran takwas ga watan Mayun 2011.
Jaddawalin farko ya tanadi shirya zaɓɓuɓkan ´yan majalisa da na ƙananan hukumomi kamin ƙarshen shekara da mu ke ciki.
Baki ɗaya, mutane miliyan huɗu da rabi ne, ya cencenta su kaɗa ƙuri´a a wannan zaɓɓuɓuka.
Mawallafi: Pinaɗo AbduEdita: Yahouza Sadissou Madobi