Hukumar EU ta bukaci yin adalci kan batun 'yan gudun hijira
September 9, 2015A jawabin da ya yi a gaban majalisar dokokin Turai da ke Strassbourg inda ya kayyade adadin 'yan gudun hijira da kowace kasa ta Turai ya kamata ta tsugunar, Jean Claude Juncker da ke zama shugaban Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai EU, bai yi barkawancin da aka sanshi da shi ba, a lokacin jawabin a kan lamarin da ya shafi 'yan gudun hijirar Siriya da ke neman mafaka. Maimakon haka ma dai ya nunar da cewar kasashen EU sun gaza tinkarar matsalar kwararar 'yan gudun hijira ta hanyar yin magana da murya gudu. Saboda haka ne Juncker yake ganin ya zama tilas kasashe 28 da ke da kujera a EU su amince da matakin rarraba 'yan gudun hijirar Siriya tsakaninsu.
"Muna bukatar hada karfi a kan manufar da ta shafi gudun hijira. Gaskiyar ita ce duk abubuwan da suka shafi gudun hijira da kuma bayar da mafakar siyasa na bukatar daukar mataki na din-din-din daga garemu. Saboda haka ne yanzu Kungiyar Tarayyar Turai ta yunkura inda ta yi tayin matakin rarraba 'yan gudun hijira, domin mu samu damar magance irin wannan matsala idan ta taso nan gaba."
Kokarin samun mafita daga batun 'yan gudun hijira
Shugaban na Hukumar ta EU ya yi kira ga mambobin kungiyar da su dauki matakin gaggawa na tsugunar da 'yan gudun hijira dubu 160 da ke watangaririya yanzu haka.
A ranar Litinin mai zuwa ne dai ministocin harkokin wajen Turai za su gudanar da taron musamman a Brusseles kan batun na gudun hijira. Idan za a iya tunawa dai an tashi baram-baram a taron da ya gudana a watan Yuni kan rabon 'yan gudun hijira 400 tsakanin kasashen EU sakamakon adawa da kasashen Turai ta Gabas da Birtaniya da kuma Spaniya suka nuna. Saboda haka ne Jean-Claude Juncker ya ce ya kamata su yi alfahari da tururuwa da 'yan gudun hijira ke yi don neman mafaka a Turai, ya na mai cewa alama ce ke nuna cewar wannan nahiya na zaman lafiya, kana tana da ci gaban tattalin arziki.
"Ina goyon bayan matakin ba wa masu neman mafaka izinin aiki domin su samu damar rike kansu maimakon bas u taimako. Aiki ne ke ba wa mutum damar yin alfahari. Wadanda suke aiki na dawo da mutuncin da aka sansu da shi a baya. Saboda haka mu dauki matakan da suka dace don canja dokokinmu domin ba wa 'yan gudun hijira izinin yin aiki tun ranar farko da suka iso Turai."
Manufa ta bai-daya kan 'yan gudun hijira
Jean-Claude Juncker ya ce miliyon 'yan Turai sun taba samun kansu cikin hali na gudun hijira a shekarun baya. Sannan kuma a yanzu tana da karfin da za ta tsugunar da wadanda ke gudun kasarsu don yaki da cin zarafi. Saboda haka ne ya bukaci a karkasa 'yan gudun hijira tsakanin kasashen na EU tare da yin la'akari da karfin tattalin kowacce daga cikinsu.
Kasar Jamus ce dai za ta dibi kaso mafi yawa, sai kuma Austriya da kuma Beljium. Sai dai kuma Juncker ya ce a yi hattara game da bakin haure da za su nemi yin amfani da matsalar gudun hijira wajen cimma burinsu na shigowa Turai.
"Hadaddiyar manufa kan gudun hijira da mafakar siyasa na bukatar tsayawa tukuru don kare iyakokinmu. A Kungiyar Tarayyar Turai mun soke shingaye da ke tsakaninmu don ba wa jama'a damar yin walwala. Wannan muhimmin mataki ne na hadin kanmu, sannan ina tabbatar muku cewar ba za a soke wannan mataki karkashin wa'adin shugabanci na ba."
'Yan majalisar Turai da ke da ra'ayin jari hujja sun yi na'am da matakin rarraba 'yan gudun hijira tsakanin kasashen EU. Sai dai wadana aka zaba karkashin jam'iyyun da ke kyamar baki suka ce EU na neman mayar da nahiyar inda kowa zai iya shigowa lokacin da ya ga dama.