1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar IAEA ta ce Iran ba barazana ba ce a huskar makaman nukiliya.

May 31, 2006
https://p.dw.com/p/Buw2

Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta ƙasa da ƙasa, Mohamed El Baradei, ya ce a halin da ake ciki yanzu dai, Iran ba wata barazana ba ce a huskar makaman nukiliya. Da yake jawabi a wani taron ƙasa da ƙasa a birnin San Francisco a Amirka, El Baradei ya gargaɗi gamayyar ƙasa da ƙasa da ta yi taka tsantsan wajen tinkarar wannan batun, don kada maimaita kurakuran da aka yi a kan batun Iraqi da kuma Korea Ta Arewa.

Ya kuma ƙarfafa cewa, ya tabbatar mafi yawan shugabannin Iran ɗin na sha’awar ganin an warware wannan matsalar ne ta hanyar diplomasiyya. A halin da ake ciki dai, ƙasashe guda 5 masu zaunannun kujeru a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Jamus na shirin gudanad da wani sabon taro a birnin Vienna a ran alhamis mai zuwa, don tsara wani sabon tayin da za su yi wa Iran, a yunƙurinsu na shawo kanta ta dakatad da shirin sarrafa sinadarin yureniyum, ko kuma idan ta ƙi su sanya mata takunkumi.