Hukumar IMF za ta tsame hannu daga shirin ceto Girka
July 30, 2015Hukumar bada lamuni ta duniya ta IMF ta ce ba za ta shiga cikin shirin tallafa wa kasar Girka domin ceto ta daga matsalar bashinta ba matsawar Girkan da kanta ba ta amince ta aiwatar da illahirin matakan tsuke bakin aljihun da aka gindaya mata ba, matsawar kuma kasashen Turai ba su cimma matsaya daya ba ga rage bashin da suke bin kasar ta Girka.
Wani daga cikin shugabannin hukumar ta IMF ne ya bayyana hakan a wannan Alhamis inda ya ce sai idan wadannan sharudda biyu sun cika ne kadai hukumar za ta ba da hadin kanta ga shirin ceto kasar ta Girka.
A share daya kuma firaministan kasar ta Girka ne Alexis Tsipras ya yi barazanar sake shirya wani zaben raba gardama a ranar Lahadi mai zuwa kan batun, matsawar shirin nasa zai ci gaba da fuskantar tarnaki daga jam'iyyarsa da ke ci gaba da nuna adawarsu da matakin tsuke bakin aljihun da gwamnatin kasar ta amince da shi.