1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar INEC ta dage zabe a Najeriya

Yusuf Bala Nayaya
February 15, 2019

A ranar Asabar ‘yan Najeriya suka so fita kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na majalisun kasar biyu, yanzu dai sai ranar 23 ga watan na Fabrairu.

https://p.dw.com/p/3DT9H
Nigeria - Verschiebung der Präsidentschaftswahlen
Farfesa Mahmood Yakubu shugaban hukumar zaben Najeriya ta INECHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta dage zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa da aka tsara za a yi a wannan rana ta Asabar, abin da ke ke zuwa sa'oi kafin bude tashoshin kada kuri'ar. Dukkanin manyan jam'iyyu biyu na kasar dai sun zargi juna da cewa dagewar shiri ne na tsara magudin zabe.

Da misalin karfe bakwai na safiyar nan ne dai aka so fara zaben a tashoshin  kada kuri'a 120,000 a wannan kasa da ke kan gaba da yawan jama'a a nahiyar Afirka. Wacce za ta yi zabe da 'yan takara 73 a kan takardar kada kuri'a.
Shugaba Muhammadu Buhari dan shekaru 76 na neman wa'adi na biyu na mulkin kasar inda yake fuskantar kalubale daga madugun adawa kuma tsohon matauimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar dan shekaru 72.

Nigeria Präsidentschaftswahl 2015
Kai kayan zabe na kan gaba a dalilan dage zabenHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Tun cikin daren Juma'a aka shiga rade-radin cewa za a dage zaben na Najeriya bayan da aka fahimci kayan aikin zaben da suka hadar da takardar kada kuri'a ba ta kai ga yankuna da dama ba da za a yi zaben. Lamarin da ya sanya shugaban hukumar zaben mai zaman kanta a Najeriya INEC Mahmood Yakubu ya kira taron gaggawa na jami'an hukumar lamarin da ya sanya suka dage zaben nan da mako guda mai zuwa wato ranar 23 ga watan nan na Fabrairu.