Hukumar zabe mai zaman kanta ta tabattar da Ellen Johson a matsayin shugabar kasar Liberia
November 23, 2005Hukumar zabe mai zaman kanta a kasar Liberia, ta bayana Madame Ellen Sirleaf Johson ,a matsayin wadda ta lashe zaben shugaban kasa zagaye na 2.
Sakamakon karshe da shugabar hukmumar zaben, Frances Morris Johson, ta bayyana yau laraba, a birnin Monrovia,y ace Ellen Sirleaf ta ci nasara da kashi 59 dadugu 4 bisa 100 a yayin dad an takara na 2 Jeorges Woyah ya samu kashi 40 da dugu 6 bisa 100 na daukacin kuri´un da a ka kada.
Sakamakon bai cenza ba, da na farko, da hukumar ta bayyana kwanakin baya.
Dan takara Georges Woyah ya yi korafin cewar an tabka magudi, saidai a binciken da hukumar ta gudanar ta gano cewa zargin ba shi da tushe.
Tunni dai, kasashen dunia, da kungiyoyin kasa da kasa, da su ka hada da Kungiyar taraya Afrika, da ECOWAS kokuma CEDEAO, sun aika sakwanni taya murna, ga sabuwar shuagabar Liberia sun kuma yi kira ga Georges ya yi hakuri da abun da Allah yayi, ya kuma bada hadin kai, domin sake gina kasar Liberia, da yaki ya daidaiata, a tsawan shekaru masu yawa.
Madame Ellen Sirleaf, yar shekaru 67 a dunia, na matsayin mace ta farko, da ta hau kujera shugabacin kasa a tarihin Afrika.