Hukumar zabe ta bayyana wadanda za su yi takara a Najeriya
October 26, 2018Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta sanar da cewa mutane 79 ke takarar neman shugabancin kasa a zaben da za a yi a badi, inda ta wallafa takardunsu domin duk mai korafi ya nufi kotu, to sai dai ta jadadda cewa jamiyyar APC bata kai mata sunayen ‘yan takara daga jihar Zamafara ba, a yayainda lamarin ke kotu.
A bisa jadawalin tsare-tsaren da hukumar zaben ta fitar tun daga ranar 9 ga watan Janairun bana na gudanar da babban zaben a badi, wanda ya nuna matakai 14 da za a aiwatar, ya zuwa yanzu hukumar tace an aiwatar da guda uku da suka hada da wallafa sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da na ‘yan majalisun dattawa da na wakilai a Najeriya. Hakan na kunshe ne cikin tsarin mulkin kasa, domin masu korafi a kan takardun da ‘yan takarar suka gabatar.
Duk da kaiwa ga wannan mataki a shirye–shryen zaben, har zuwa yanzu ana fuskantar takaddama sosai a kan batun ‘yan takara na jam‘iyyar APC, musamman a jihar Zamfara.
Akwai dai korafe-korafe da dama a game da batun ‘yan takara na jamiyyar APC daga jihohi da daman a kasar, abin da Usman Tugga, daya daga cikin ‘yan takarar da ake takaddama a zaben fidda gwani a jihar Bauchi ya ce shi ya nufi kotu.
A yayin da ya rage kwanaki 112 a gudanar da zaben na Najeriya a shekara mai kamawa, hukumar zaben ta ce tuni ta yi nisa wajen tanadin yadda za ta aiwatar da dokar zaben da aka yi wa gyaran fuska da zaran shugaban Najeriya ya sanya mata hannu.