1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da hukumar zaben kasar Chadi

Gazali Abdou Tasawa
April 4, 2019

Mambobin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Chadi wato Ceni sun sha rantsuwar kama aiki a wannan Alhamis a gaban kotun kolin kasar wannan kuwa duk da rashin amincewar jam'iyyun adawar kasar da ita

https://p.dw.com/p/3GF3i
Wahlen Tschad Wahlhelfer
Hoto: Getty Images/I. Sanogo

A kasar Chadi, mambobin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar wato Ceni su 31 sun sha rantsuwar kama aiki a wannan Alhamis a gaban kotun kolin kasar wannan kuwa duk da rashin amincewar jam'iyyun adawar kasar da kasafin mutanen da hukumar zaben ta kunsa.

 A lokacin shan rantsuwar dai mamabobin hukumar zaben, wacce za ta shirya zabukan 'yan majalisa da na kananan hukumomi, sun sha alwashin yin aiki a cikin gaskiya da adalci, sai dai kuma 'yan adawar sun bayyana hukumar a matsayin haramtatta. 

A hakumance dai hukumar zaben ta kunshi mambobi 15 daga bangaren masu mulki, 15 daga bangaren adawa, sai dai 'yan adawar na cewa mutanen da aka nada da sunansu ba su suka wakilta su ba. Ko a ranar Litinin da ta gabata dai jam'iyyar adawa ta UNDR ta Saleh Kibzabo wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasa na 2016 ya yi kira da a soke kudirin da ya kafa wannan hukumar zabe. 

Sai dai tuni wasu manyan kasashen duniya kawayen kasar ta Chadi kamar su Faransa suka sanar da daukar nauyin shirya wadannan zabuka wanda za a gudanar a watan Mayu na wannan shekara.