Hukumomin Iran na fuskantar yawan takunkumi
December 14, 2012
Fadar Amurka ta kara lakabawa kasar Iran wani takunkumi a dangane da manufofin kasar na shirin nukleya.
Ofishin da ke kula da baitulmanin kasar ta Amurka ta bakin kakakinsa,ya ce ya kara azawa wasu jami'ai da kamfanonin Iran din takunkumi wadanda suka hada da kamfanoni 7 na kasar da kuma babban jami'in kula da shirin makamashin kasar,wanda ya ketare rijiya da baya a wani yunkurin halaka shi da aka yi wanda kuma hukumomin na Iran suka alakanta da kasar Isra'ila.
kasashen duniya dai na ci-gaba da nuna damuwarsu a kan shirin makamashin kasasr da suka danganta da na yunkurin kera makaman nukleya ne,zargin da hukumomin kassar ke musantawa.
A jiya Alhamis ne dai jami'an hukumar makamashi ta Duniya suka bar kasar bayan wata ziyarar da Iran din ta bayana gamsuwarta a kanta.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Saleh Umar Saleh