Ana ci gaba da tsare dan jaridar Al Jazeera a Berlin
June 22, 2015Gwamnatin Jamus ta ce ta tsare dan jaridar nan na tashar Al Jazeera kuma dan kasar Masar Ahmed Mansur bisa wani sammacin kame shi da hukumar 'yan sandan duniya Interpol ta bayar tun a cikin watan Oktoban shekarar 2014. Bayanai daga ma'aikatar harkokin wajen Jamus sun nunar cewa ba an kame shi ne saboda hukuncin da Masar ta yanke masa, akwai kuma wasu tuhume-tuhume na daban. Kakakin ma'aikatar Martin Schäfer ya ce za a gudanar da cikakken bincike. A shekarar 2014 wata kotu a birnin Alkahira ta yanke wa Mansur hukuncin daurin shekaru 15 a bayan idonsa, saboda laifi da hannu a cin zarafin wani lauya. Abin da ya shige wa mutane duhu shi ne mai yasa sai a ranar Asabar aka kama dan jaridar lokacin da ya zo tashi daga filin jirgin saman birnin Berlin. Lauyansa ya ce tun a tsakiyar watan Yuni ya isa birnin Munich ta jirgin sama. Tuni dai kungiyar 'yan jaridun Jamus da ma daukacin jam'iyyun siyasar kasar suka yi gargadi game da tasa keyarsa zuwa Masar.