1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin kasar Girka na ci gaba da ziyara a Turai

February 3, 2015

A wannan Talata sabbin magabatan kasar Girka za su isa birnin Rome na kasar Italiya, a wani rangadi da suka soma a kasashen Turai don samun goyon baya.

https://p.dw.com/p/1EUmY
Hoto: picture-alliance/dpa

Yayin da yake ziyara a birnin London, ministan kudin kasar ta Girka Yanis Varoufakis ya ce babu wani bata lokaci, kuma ko wadanne mintoci suna da nasu mahimmanci a cikin wannan kokowa da suka sama gaba ta neman a y musu rangwame game da bashin da ke kan kasar. Gwamnatin ta Girka dai ta soma wannan rangadi ne a kasashen Turai, tun daga karshen makon da ya gabata, domin gamsar da kasashen ta yadda za su sassauta mata halin kuncin da take fama da shi a fannin tattalin arziki. Bayan da ya ziyarci birnin Paris, sabon ministan kudin kasar ya je birnin London na kasar Birtaniya, kafin ya wuce tare da tawagarsa ya zuwa birnin Rome na Italiya a wannan Talatar.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal