1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin Masar sun tsare mutane da yawa karkashin dokar yaki da ta'addanci

December 26, 2013

Tun bayan harin kunar bakin wake da aka kai kan wata shelkwatar 'yan sanda da ke birnin Mansura, mahukuntan birnin Alkahira ke matsa lamba kan masu kishin Islama.

https://p.dw.com/p/1AhDt
Hoto: Reuters

Gwamnatin Masar na kara matsa kaimi a kan kungiyar 'Yan uwa Musulmi, inda a wannan Alhamis ta tsare akalla mutane 38 bisa zargin kasancewa 'ya'yan wata kungiyar 'yan ta'adda. Bayan fashewar wani karamin bam da ya raunata mutum biyar a birnin Alkahira, Janar Abdel Fatah Al-Sisi wanda ya jagoranci juyin mulkin da aka yi wa shugaba Mohammed Mursi a cikin watan Yuli da ya gabata, ya ce kasar za ta tashi haikan don yakar ta'addanci. A ranar Laraba gwamnati ta ayyana kungiyar 'Yan uwa Musulmi a matsayin kungiyar 'yan ta'adda biyo bayan wani harin kunar bakin wake da ya halaka mutane 16 a yankin Nile Delta ranar Talata da ta gabata, wanda gwamnati ta zargi 'Yan uwa Musulmi da hannu a ciki, ko da yake kungiyar ta musanta zargin kana ta yi tir da harin.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman