Turkiyya ta zargi IS da kai harin filin jirgin sama
June 29, 2016Wasu 'yan kunar bakin wake uku sun bude wuta tare da tashin bama-bamai da ke a jikinsu a filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Santambul na Turkiyya, abin da ya yi sanadi na kisan mutane 36 da raunata kimanin mutane 150. Firaminista Binali Yildirim na kasar ta Turkiyya ya bayyana lamarin da cewa hari ne irin na mayakan 'yan ta'adda daga kungiyar IS.
Ya ce: "Kawowa yanzu bayanan da aka tattara mutane 36 ne suka rasu tare da 'yan kunar bakin waken uku, an samu mutane da dama da suka samu raunika wasu kadan wasu mai yawa ana basu kulawa."
Daya daga cikin maharan dai ya bude wuta ne a sashen filin jirgi da fasinjoji masu tafiya ke taruwa kana daga bisani tare da sauran 'yan kunar bakin waken da ke a sashen da fasinja ke shiga filin tashi da saukar jiragen saman suka tashi ababan fashewar da ke jikinsu.
Harin na filin jiragen sama na uku mafi girma da yawan jama'a a duniya na zama daya daga cikin mafiya muni cikin jerin hare-hare da ake kai wa kasar ta Turkiyya, wacce ke zama daya daga cikin kasashe da ke kawance da Amirka a yaki da 'yan ta'adda na kungiyar IS, wadanda ke neman fantsama zuwa kasar yayin da daga Kudu maso Gabashin kasar ake fama da hare-hare na mayakan sakai na Kurdawa.