1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Rasha: An kulle dan adawa Oleg Orlov a gidan kurkuku

Abdourahamane Hassane
February 27, 2024

Wata kotu a Rasha ta yanke wa dan adawa Oleg Orlov, mai kare hakkin dan Adam hukuncin daurin shekaru biyu da rabi na zaman gidan yari,saboda ci gaba da yin Allah wadai da harin da sojojin Rasha ke kai wa Ukraine.

https://p.dw.com/p/4cw9Q
 Oleg Orlow
Oleg OrlowHoto: Tatyana Makeyeva/REUTERS

Daruruwan jama'a ne suka je kotu domin mara Orlov baya, wanda yake da shekaru 70 a duniya, kuma yana daya daga cikin masu sukar lamirin gwamnatin da ya yi tsayin dakka a Rasha ba tare da ficewa ba daga kasar zuwa hijira. A ƙarshen shekara ta  2021, 'yan makonni kafin harin Rashar ta kai wa Ukraine, gwamnatin Vladmir Putin ta haramta kungiyarsa NGO memorial wacce ta samu lambar yabo ta zaman lafiya ta  Nobel.