Hukuncin daurin shekaru 20 wa Dadis Camara
July 31, 2024Haka kuma daga cikin laifukan da aka samu mutanen da aikatawa, baya ga kisan mutanen an samu sojojin da laifin fyade ga masu gangamin siyasa a 2009. Kotun hukunta manyan laifuka ta kasar Gini, ta yanke hukuncin wa Moussa "Dadis" Camara da wasu manyan jami'an gwamnatinsa bakwai hukuncin aikata manyan laifuka da suka hada da kisan kai, yin fyade, yin garkuwa da mutane da duk aka bayyana su a matsayin manyan laifuka na keta hakkin dan Adam. Sama da mutane 100 wadanda suka tsira daga farmakin sojojin da kuma iyalan wadanda suka mutu suka bada shaidar abin da ya faru a shari'ar da aka fara tun shekaru biyu da suka gabata, shari'ar da aka yi ta jan kafa a kanta, amma kuma daga karshe a wannan Laraba an kai ga yanke hukunci. A lokacin shaidu suka ce wasu mutanen an hallaka su da yankan wuka, wasu da bindiga, wasu matan kuwa an yi ta masu fyade har suka mutu, yayinda wasu sojoji na Gini suka sace mata suka boyesu a lokacin suka yi ta musu fyade.