Hukuncin kisa a kan mutane 16 a Saudiyya
October 22, 2015A Saudiyya babban mai shigar da kara na kasa ya yanke hukuncin kisa ga wasu mutane 16 da ake zargi da aikata ayyukan ta'addanci a wani gari mai suna Awamiya da ke da rinjayen mabiya tafarkin Shi'a a kasar.
Uku daga cikin wadannan mutane na cikin jerin wasu mutane 23 da hukumomin Saudiyyar ke nema ruwa a jallo a bisa zarginsu da kasancewa masu hannu a cikin wata zanga-zangar neman kawo sauyi a kasar da ta gudana a shekara ta 2011 a daidai tsakiyar boren juyin juya hali da aka gudanar a wasu kasashen Larabawa.
Kungiyar kare hakin dan Adam ta kasar ta Saudiyya ta ce uku daga cikin mutanen da wannan hukunci na kisa ya shafa yara ne 'yan kasa da shekaru 18 a lokacin da aka kamasu. Tuni dai kasashen duniya suka soma gudanar da kiraye kiraye na neman a yi jin kai ga wadannan yara wadanda afuwar Sarki Salmane na Saudiyyar ce kadai ka iya cetosu daga wannan hukunci na kisa.