1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin rataya a Pakistan

Yusuf BalaAugust 4, 2015

"Me yasa suka rataye ɗan uwana, saboda kawai mu talakawa ne, Allah ne zai saka mana" A cewar Sumaira Bibi 'yar uwa ga Hussein.

https://p.dw.com/p/1G9J3
Pakistan Eltern Shafqat Hussain Hinrichtung
Mahaifan Shafqat HusseinHoto: Getty Images/AFP/S. Qayyum

Ƙasar Pakistan a ranar Talatan nan ta rataye mutumin da hukuncin da aka yanke masa ya ɗauki hankalin ƙasa da ƙasa, bayan da lauyan da ke ba shi kariya ya bayyana cewa wanda yake karewa ya amince da aikata kisan yaro ne bayan da ya sha tuhuma cike da shan matsa da duka. A cewar wani jami'i a wata cibiya da ke fafutikar kare hakkin dan Adam a ƙasar ta Pakistan ya ce an rataye Shafqat Hussein a safiyar Talatan nan a birnin Karachi , duk da kiraye-kirayen kasa da kasa na a dakatar da kisan.

A cewar Lauyan da ke kare Hussein bayanai da ya tattara sun nunar da cewar Hussein na da shekaru 17 ne lokacin da aka kama shi a shekarar 2004 inda bayan konashi da taba sigari da zare masa farata, wahala ta sanya ya ce ya aikata kisan wani ƙaramin yaro.Tuni dai iyalin mamacin suka ce ba a yi musu adalci ba kan wannan hukunci.