Hukuncin kotin Karlsruhe game da Euro
September 12, 2012Babbar kotin tsarin mulkin tarayya Jamus, dake birnin Karlsruhe, ta yanke hukunci game da cece-kucen da fasalin ceto tattalin arzikin ƙasashen Turai ya jawo.
Jamusawa da dama, gami da wasun 'yan majalisar tarayya, suka shigar da ƙara, domin ƙalubalantar fasalin ceto kudin Euro da tattalin arzikin ƙasashen tarayya Turai da ya kama hanyar wargajewa.
Wanda suka shigar da ƙaran, sun yi ƙorafin cewa wannan fasali ya saɓawa kundin tsarin mulkin Tarayya Jamus.
A yayin da ya ke baiyana sakamakon hukuncin da suka yanke,babban alƙalin kotin, Andreas Voßkuhle na cewa:
"Bayan dogon nazari, mun haƙiƙance wannan fasali bai saɓawa tsarin mulkin tarayya Jamus ba."
Voßkuhle, ya ba shugaban ƙasar Jamus izinin rattaba hannu kan wannan tsarin ceto,saidai ya gitta wasu sharruɗa.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da sauran takwarorinta na ƙasashen Turai, sun yi Allah san barka da wannan hukunci.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita:Usman Shehu Usman