Kotu ta yanke hukunci kan tekun China
July 12, 2016Talla
Kotun da ta saurari karar takaddama da ake yi a tsakanin kasashen da ke da iyaka da tekun Kudancin China ta bayyana cewa mahukuntan kasar ta China ba su da iko na ci gaba da mamayar yankin tekun na Kudancin Sin, kuma ma ko da a tarihi ba ta da iko na mallakar wannan yanki. Har ila yau wannan kotu da ke a birnin Hague ta kara da cewa abubuwan da kasar ta China ke yi na mamayar, musgunawa ce ga mahukuntan kasar Pilipin. Tuni dai mahukuntan na Beijing suka bayyana hukuncin da zama cin fuska a gare su.