Hukuncin kotun duniya a kan Charles Taylor
May 30, 2012Talla
A wannan Laraba kotun ƙasa da ƙasa ta birnin The Hague take yanke hukunci a kan tsohon shugaban ƙasar Laberiya Charles Tayor wanda aka same shi da aikata laifin yaƙi. Babban alƙalin kotun musamman akan laifukan yaƙi da aka aikata a ƙasar Saliyo, Richard Lussick zai sanar da hukuncin. A ranar 26 ga watan Afrilu aka tabbatar da laifukan yaƙi da cin zarafin bil Adama a kan tsohon shugaban na Laberiya. Babbar mai shigar da ƙara ta kotun Brenda Hollis na bukatar a yanke wa Taylor hukuncin ɗaurin shekaru 80 a kurkuku. A cikin watan Maris aka kammala shari'ar da ake wa Taylor wadda aka ɗauki shekaru huɗu ana yi.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman