Hukuncin kotun koli kan zaben Ganduje da Tambuwal
January 20, 2020Ra'ayi dai ya zo daya a tsakanin alkalan kotun guda Bakwai kamar yadda mai shari'a Sylevester Ngwuta da ya karanta hukuncin cewar ba hujjar karbe zabe daga hannun Ganduje a Kano.
Jam'iyyun biyu ne dai ke mulki a jihohin kafin kaiwa ga wani hukuncin da ya kwace gwamnatin jihar Imo da ya tada hankali a daukacin kasar.
Hukuncin dai ya kawo karshen doguwar takkadama a jihohin guda biyu da ke zama masu tasiri a sashen arewacin kasar. Barrister Ibrahim Muktar kwamishinan shari'ar jihar Kano kuma daya daga cikin lauyoyin Ganduje yace hukuncin ya yi musu daidai kuma dama abin da ya dace kenan.
A nasa bangaren Barrister Husainin Umar Tudun Wada daya daga cikin lauyoyin Abba Kabir Yusuf yace babban darasi na zaman hade kan mutanen jihar ba tare da tunanin ramuwar gayya ba.
To sai dai kuma a fadar Barrister Sunusi Musa da ya kalli shari'un guda uku akwai banbanci a tsakanin hukuncin Imo da hukuncin Kano.
Can ma a Sokoto ranar na zama ta murna ga magoya bayan gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal da kotun ta ce shine halastaccen gwamna a jihar.