1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin Togo game da yunƙurin juyin mulki

September 15, 2011

Kotun ƙolin Togo ta sami Kpatcha Gnassingbe da ke zama ɗan uwan shugaban ƙasa da laifin yunƙurin kifar da gwamnati, tare da yanke masa hukuncin shekaru 20 a gidan yari.

https://p.dw.com/p/12Zx2
Shugaba Faure Gnassingbe na Togo da aka yi yunƙurin kifar da gwamnatinsaHoto: DW

Kotun ƙolin ƙasar Togo ta yanke wa ɗan uwan shugaba Faure Gnassingbe hukunci shekaru 20 a gidan yari bayan da ta same da shi da laifin yunƙurin juyin mulki shekaru biyun da suka gabata. Shi dai Kpatcha Gnassingbe mai shekaru 41 da haihuwa ya taɓa rike muƙamin ministan tsaron Togo, kana ya na ɗaya daga cikin 'yayan tsohon shugaban wannan ƙasa Marigayi Gnassingbe Eyadema.

Shi ma dai tsohon hapsan hapsoshin sojojin ƙasar wato janar mai ritaya Assani Tidjani da kuma wasu manyan jami'ai, an yanke musu hukunci watanni 20 zuwa shekaru 20 a gidan waƙafi. yayin da shi kuma ɗan uban shugaban ƙasa wato Essolizam Gnassingbe, aka yi masa ɗaurin talala na watanni 24.

A farkon wannan wata na satumba ne dai aka fara shari'ar manyan sojojin ƙasar da kuma manyan jami'ai na gwamnati da ake zargi da marar hannu wajen kitsa juyin na mulki. Har ya zuwa yanzu dai hukumomin Lome ba su yi ƙarin haske ba game da takamaimen abin da ya afku ba lokacin da Kpatcha Gnassingbe ya yi wannan yunƙuri a watan afrilun 2009 ba, lokacin da shugaban ƙasar Togo Faure Gnassingbe ke niyar gudanar da ziyarar aiki a ƙasar China.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Mohammad Nasiru Awal