Huldar Rasha da Siriya
June 18, 2016
Gidan talabijin din gwamnatin Siriya bai yi wani karin haske ba kan ziyar bazata da Sergei Shoigu ya kai Damaskus, sai dai an bayyana cewa ministan tsaron na Rasha ya je Siriya ne bisa umarnin shugaba Vladimir Putin. Don karfafa tsare-tsaren aiki tare tsakanin sojojin Siriya da na Rasha, ta yadda za su ci gaba da fatattakan 'yan ta'adda.
Birnin Aleppo dai yana daga cikin inda hankali ya fi karta a rikicin na Siriya, inda wannan mutumin ke cewa.
"Jiragen yaki sun kai farmaki a anguwar Fardous da safiyar yau. da kuma anguwannin Bstan al Qaser da Bab al Nairab. Da sanyin safiya sai muka ji makamai masu linzami na sauka. Harin ya ritsa da mutane cikin buraguzai, amma dai mun gode wa Allah domin duk mun zakulo su".
A 'yan kwanakinnan dai gwamnatin Siriya na ci gaba da yin galaba kan 'yan tawaye da 'yan ta'adda, wannan kuwa godiya ta tabbata ga tallafin kasar Rasha.