Dubai: Barazanar kai hari daga Huthi
September 18, 2019Mayakan na Huthi dai sun ce biranen da ke barazanar fuskantar hare-haren daga gare su sun hadar da Dubai da sauran manyan birare. A wani Labarin kuma yarima mai jiran gado na Saudiyyan Mohammed bin Salman ya shaidawa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho cewa suna son a gudanar bincike daga al'ummomin kasa da kasa kan harin da 'yan tawayen na Huthi suka dauki alhakinsa, amma Saudiyyan da Amirka suka zargi Iran da kaiwa. Rahotanni sun nunar da cewa tuni jami'an Majalisar Dinkin Duniya suka kama hanyarsu ta zuwa Saudiyyan domin gudanar da bincike. Da yake mayar da martani kan takunkumin da Amirka ta sake kakabawa kasarsa, ministan harkokin kasashen ketare na Iran da Amirka da Saudiyya ke zargi da kai hari a Saudiyya, Mohammad Javad Zarif ya bayyana matakin da yakin tattalin arziki kan al'ummar Iran.