I S ta sake kwace iko da yankuna a Siriya
November 10, 2017Talla
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Sojojin gwamnati suka yi ikirarin mallake yankunan 'yan tawayen, kungiyar kare hakkin bil adama ta Syrian Observatory for Human Rights, ta ce bangarokrin biyu sun gwabza kazamin fada ta hanyar musanyar wuta a Deir al-Zour da ke da arzikin man fetur.
A yanzu 'yan tawaye sun samu damar karbe kashi 40 cikin dari na yankin al-Bu Kamal da ke kusa da kan iyaka da kasar Iraki, to sai dai wannan kwan gaba kwan bayan na zuwa ne a dai-dai lokacin da wasu rahotanni ke nuna bayyanar shugaban kungiyar ta I S Abu al-Baghdadi a a garin Albu Kamal da ke Siriyar.
Amma rahoto da mayakan Hezbollah suka fitar, bai bayyana ko an kama Baghadadi a gumurzun wuta tsakanin mayaka da sojoji a kan iyakar Siriya da Irakin ba.