Farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran
March 3, 2022Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya IAEA din dai ta ce, tna son ganawar kai tsayen ne domin ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran din da aka cimma tun a shekara ta 2015 kuma har yanzu ake ta cece-kuce a kanta. Rafael Grossi dai na fatan ganawa da manyan jami'an gwamnatin Iran din a Tehran babban birnin kasar, ranar Asabar mai zuwa. Tehran din dai ta bukaci hukumar ta IAEA ta dakatar da binciken ayyukan nukiliyarta na sirri da ta yi a baya, batun kuma da ke zaman guda daga cikin abubuwan da har yanzu ke kawo tarnaki wajen kammala farfado da yarjejeniyar ta 2015 da ke tangal-tangal. Akwai dai matukar wahala a iya kai wa gacci wajen farfado da yarjejeniyar nan ba da jimawa ba, duk da cewa an tattauna batun janyewa Tehran sababbin takunkuman da Amirka ta sanya mata da kuma batun sanya sababbin dokoki ga Iran din kan shirinta na nukiliyar.