1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IAEA ta zayyana sabon kuduri kan Iran

November 17, 2011

Hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa(IAEA) ta zayyana sabon kuduri akan shirin nukiliyar Iran da ba shi kunshe da wa'adin mai da martani

https://p.dw.com/p/13CYT
Shugaba Mahmoud Ahmadinejad, a tsakiya yayin ziyara a tashar nukiliyar NatanzHoto: AP

A cikin kudurin da ta zayyana akan shirin nukilyar Iran hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA ba ta bai wa Iran waadin mai da martani game da sabon rahoton da ta fitar akan shirin Iranta na nukiliya ba. A maimakon haka kudurin da gaggan kasashen duniya ke aiki akai a hukumar kira yayi ga shugabanta Yukia Amano da ya ba hukumar labarin duk wani ci gaban da aka samu a tattaunawar da ake yi da Iran. Wakilin Israila a hukumar ya nuna rashin jin dadinsa da yake sa rai yai cewa rahoton da hukumar IAEA ta fitar a wancan mako akan zaton da ake cewa Iran na da manufar kera makaman nukiliya zai janyo zazzafan martani daga komitin dake kula da aikin hukumar ta IAEA.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu