1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ibrahim Gambari zai koma ƙasar Burma ko Myanmar a yau

November 3, 2007
https://p.dw.com/p/C155

A yau asabar ake sa rai jakadan MDD na musamman Ibrahim Gambari zai isa a Rangoon babban birnin kasar Burma ko Myanmar inda zai tattauna da shugabannin gwamnatin mulkin sojin kasar. Ziyarar ta sa ta bzo ne kwana guda bayan da gwamnatin sojin ta sanar da cewa ba zata sabunta izinin zama ga babban jami´in MDD a birnin Rangoon ba wato Charles Petrie. A cikin wata sanarwa da ya bawa MDD a watan da ya gabata mista Petrie ya yi tir da abin da ya kira tarbarbarewar halin da ake ciki a Burma. Ya ce an yanke hanyoyin sadarwa na intanet sannan an takaitawa jama´a hanyoyin shiga shafukan yanar intanet ta kasa da kasa. Wannan ziyarar dai ita ce ta biyu da Ibrahim Gambari zai kaiwa Burma tun bayan murkushe zanga-zangar nuna adawa da gwamnati wadda aka fara a watan satumba bayan kara farashin man fetir.