1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ICC: Bukatar kama shugaban mulkin sojin Myanmar

Abdullahi Tanko Bala
November 27, 2024

Babban mai gabatar da kara na kotun shari'ar manyan laifuka ta duniya ICC Karim Khan a yau Laraba ya bukaci alkalan kotun su bayar da sammacin kama shugaban gwamnatin mulkin sojin Myanmar bisa aikata manyan laifuka

https://p.dw.com/p/4nUcK
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Mayanmar Min Aung Hlaing
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Mayanmar Min Aung Hlaing Hoto: Aung Shine Oo/AP/dpa/picture alliance

Babban mai gabatar da kara na kotun shari'ar manyan laifuka ta duniya ICC Karim Khan a yau Laraba ya bukaci alkalan kotun su bayar da sammacin kama shugaban gwamnatin mulkin sojin Myanmar bisa laifukan  da aka aikata kan musulmi yan kabilar Rohingya marasa rinjaye.

Gen. Min Aung Hlaing wanda ya kwace mulki daga shugabar da aka zaba ta dimukuradiyya Aung San Suu Kyi a juyin mulkin 2021 an zarge shi da laifukan cin zarafin al'umma da azabtarwa da kuma korar yan kabilar Rohingya daga kasar.

Mutane kusan miliyan daya aka tilasta wa yin kaura zuwa kasar Bangladesh mai makwabtaka domin tsira da rayukansu, lamarin da ake gani kokari ne na kakkabe kabilar da yi musu fyade da kisa da kuma kone gidajensu.