1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ICC za ta kama Vladmir Putin

Abdourahamane Hassane
March 17, 2023

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta bayar da sammacin kamo shugaban kasar Rasha Vladimir Putin bisa zarginsa da aikata laifukan yaki a Ukraine tun bayan mamayar Rasha.

https://p.dw.com/p/4OrQs
Russland | Kongress der Union der Industriellen und Unternehmer | Wladimir Putin
Hoto: Ramil Sitdikov/SNA/IMAGO

Haka kotun ta gabatar da sammacin kama kwamishiniyar kula da kare hakkin yara ta Rashar. Kotun ICC ta kara da cewa Vladmir Putin ya aikata laifukan yaki na safara yara ba kan kaida ba daga yankunan da aka mamaye na Ukraine zuwa Tarayyar Rasha.To sai dai kakakin maiktar harkokin waje na Rasha Maria Zakharova a shafinta na Telegram ta ce: ''Hukunce-hukuncen kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ba su da ma'ana ga kasarsu, ciki har da ta fuskar shari'a saboda ta ce Moscow ba ta da wani wajibci a kan kotun.''