Binciken ICC a Falasdinu kan aikata laifukan yaki
January 16, 2015Talla
Wannan dai shi ne matakin farko a hukumance da aka dauka wanda ka iya kaiwa ga tuhumar Isra'ila kan aikata laifukan yaki a Falasdinun. Babbar mai gabatar da kara a kotun ta ICC Fatou Bensouda ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike a matakin farko mai cikakken 'yanci wanda ba nuna banbanci a ciki. A ranar daya ga wannan wata na Janairu da muke ciki ne dai mahukuntan Falasdinun suka bukaci kotun da ta gudanar da bincike kan abubuwan da Isra'ila ta aikata a yankin Zirin Gaza tun daga watan Yunin shekarar da ta gabata ta 2014, kafin washe gari su mika bukatarsu na zamowa mamba a kotun ta ICC.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal