1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Idomeni: Sake tsugunar da 'yan gudun hijira

Sulaiman Babayo/ASMay 24, 2016

Mahukuntan Girka sun fara aikin kwashe daruruwan 'yan gudun hijira a sansanin Idomeni domin kai su wasu wurare na daban.

https://p.dw.com/p/1ItgZ
Griechenland Behörden beginnen mit Räumung des Flüchtlingslagers in Idomeni
Hoto: Reuters/Y. Kolesidis

Wannan sansani na Idomeni da ke kusa da iyakar Girka da Macedonia ya kasance daya daga cikin wuraren da lamuran jinkai suka tabarbare tun lokacin da kasashen suka rufe iyakokin da bakin haure da 'yan gudun hijira ke bi domin isa kasashen Yammacin Turai.

Griechenland Flüchtlinge in Idomeni
Hukumomin Girka sun ce za su bada fifiko ga masu iyaliHoto: DW/S. Amri

Lokacin da aka fara an kwashe kimanin mutane 1000 wadanda aka saka cikin motocin safa zuwa sansanonin da aka bude kusa da birnin Thessaloniki na biyu mafi girma a kasar. Hukumomi sun ce babban abin da suka saka a gaba shi ne tabbatar da yara wadanda suke tafiya su kadai sun samu muhalli.

Tuni dai aka fara nuna gamsuwa da wannan aiki kamar yadda Anastasios Sahpakidis wakilin kamfanonin jiragen kasa ya shaidawa manema labarai inda ya ce "aikin na tafiya kamar yadda aka tsara. Mutanen sun amince ba tare da amfani da karfi ba". To sai dai mahukuntan kasar yanzu haka sun hana 'yan jarida kusantar wannan wuri da ake kwashe 'yan gudun hijirar ciki kuwa har da wakilin DW Oliver Sallet.

Cikin kwanaki goman da ke tafe ne dai gwamnatin kasar ta Girka ta ce ta na sa ran kammala aikin. Wani kiyasi da aka yi ya nuna kimanin bakin haure da 'yan gudun hijira dubu 54 ne suka makale a kasar ta Girka bayan sun tsallaka teku, inda suka gaza kai wa zuwa sauran kasashen Turai da suke bukata domin samun rayuwa mai inganci.

Idomeni Griechenland Flüchtlinge Camp
Ana amfani da jiragen kasa wajen jigilar 'yan gudun hijira Idomeni zuwa wasu wurare na dabanHoto: picture-alliance/dpa/A.Mehmet