1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Chadi: Shugaba Deby na neman karin wa'adin mulki

Abdoulaye Mamane Amadou
April 11, 2021

Shugaba Idriss Deby Itno ya yi kira ga 'yan kasar da su fito dan kada kuri'a, wanda yin hakan tamkar sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasar ya rataya masu ne.

https://p.dw.com/p/3rqMg
Präsidentschaftswahl in Tschad | Präsident Idriss Deby Itno
Hoto: MARCO LONGARI/AFP

Shugaban na kalaman ne jim kadan bayan ya jefa kuri'arsa a yayin zaben shugaban kasa da al'ummar kasar ke yi a wannan Lahadi, zaben da ya zuwa yanzu rahotanni ke cewar komai na tafiya salin alin ba tare da wata matsala ba, sai dai masu sharhi na ganin cewa ba makawa shugaban na Chadi mai neman tazarce zai lashe zaben.

Mai shekaru 68 a duniya, Deby ya shafe shekaru 30 yana mulkin kasar, tun bayan jagorantar juyin mulki a shekarar 1990.

Sai dai 'yan adawa da dama sun kaurace wa zaben suna masu ikrarin cewa zaben yana cike da kurakurai.