1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Illar takunkumi akan Iran bisa shirin nukiliya

July 17, 2012

Iran ta ce takunkumi na daga cikin matsalolin tattalin arziƙin dake addabar kasar a baya bayannan.

https://p.dw.com/p/15ZGo
An view of a heavy-water production plant, which went into operation despite U.N. demands that Iran roll back its nuclear program, in the central Iranian town of Arak, Saturday, Aug. 26, 2006. President Mahmoud Ahmadinejad declared Saturday, after the inauguration of the plant, that his nation's controversial nuclear program poses no threat to any other country, even Israel "which is a definite enemy." (AP Photo/ ISNA, Arash Khamoushi)
Sabuwar tashar nukiliya Iran a ArakHoto: AP

Shugaban majalisar dokokin Iran yayi na'am da cewar tsaurara takunkumi akan kasar na yi mata mummunar illa. Ali Larijani ya bayyana cewar kaso 20 cikin100 na matsalolin tattalin arziƙin da Iran ke fama da su na da nasaba da takunkumin aka sanyawa kasar. Sai dai ko da shike bai fayyace abinda yake nufi da hakan ba, amma wannan shi ne karon farko da wani babban jami'in gwamnatin Iran ya bayyana matsayin illar da sanya takunkumin ke janyowa kasar.

Ƙiyasin da Larijani ya yi ya zo ne makonni biyu bayan da takunkumin sayan man fetur na Iran da ƙungiyar tarayar Turai da kuma ƙasar Amirka ya fara aiki bisa ƙiyawar da Iran din ta yi na dakatar da bunƙasa shirin ma'adinin uranium na ta.

Kwararru sun yi hasashen takunkumin da ƙasashen yammacin duniya suka sanyawa Iran zai ƙara farashin shigo da kayayyaki zuwa ƙasar da kaso 20 zuwa 30 cikin 100. Kasashen na yammacin duniya dai na zargin Iran da yunƙurin ƙera makaman nukiliya a yayin da ita kuwa ta sha nanata cewar na zaman lafiya ne.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu