1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Illolin da ke tattare da hana acaba a Kano

Usman ShehuJanuary 23, 2013

Mutane miliyon guda da rabi za su rasa sana'ar su a Kano sakamakon kafa dokar hana daukar fasinja akan babur da zai fara aiki a ranar alhamis.Gwamnatin ta dauki matakin ne don magance matsalar tsaro dake addabar jihar.

https://p.dw.com/p/17QBV
Hoto: Katrin Gänsler

Mataimakin gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya yi shelar sanya dokar hana daukar fasinja a kan babur a kananan hukumomi 8 dake cikin birni inda aka fi cunkoson mutane. Gwamnatin ta ce ta dauki wannan mataki ne bisa la'akari da yadda ake yawan kai hare hare akan Babura, musamman ma harin baya bayan nan wanda aka kai kan ayarin sarkin kano Alhaji Ado Bayero, wanda har ta kai direbansa da wasu mutane suka rasa rayukansu.

Nigeria Deutscher ermordet
Babur na daga cikin ababen hawa da aka fi amfani da su.Hoto: Reuters

Sai dai matakin bai yi wa 'yan acaba dadi ba musamman ma bisa la'akari da yawan mutanen da suke ganin zasu rasa hanyar cin abincisu sakamakon wannan mataki, kamar yadda Comrade Mohammed sani Hassan shugaban kungiyar 'yan achaba na jihar kano ya bayyana. Shi ma dai wani masanin shari'a a jihar kuma lauya mai zaman kansa Barista Mohammad Lafdo cewa ya yi matukar matakin ba na masalahar mutane bane, to fa 'yan kungiyar suna iya kalubalantar matakin a gaban kuliya.

Yan acaba da dama ciki har da Musa Ibrahim ne dai ke bayyana rashin jin dadinsu bisa wannan mataki wanda suke cewar babbar barazana ce ga rayuwarsu. Ya na mai cewa ba wai kawai 'yan achaba ya shafa ba a'a. Amma dai galibi mutanen jihar kano dan kan yi amfani da babur wajen kai 'yayansu makaranta da kuma kai iyali unguwa. Gwamnati ta ce matakin na wucin gadi ne amma babu tabbacin lokacin soke dokar.

DW_Nigeria_Integration-online3
Dalilan tsaro sun sa an hana goyo a babur a Kano.Hoto: Katrin Gänsler

Rahotanni cikin sauti na kasa

Mawallafi: Nasiru Salisu zango
Edita: Mouhamadou Awal