Illolin sauyin yanayi cikin hotuna
Matsalar sauyin yanayi ta tsananta hadarin fadawa cikin mummunan iftila'i a fadin duniya. Damana da kaka maras tabbas sun haifar da ambaliya da gobarar daji da zafi da fari da ba a taba ganin irinsu ba.
Ruwa mai tsanani a Afirka ta Kudu
A watan Afrilu, ruwan sama mai tsanani ya afku a gabashin Afirka ta Kudu, tare da haddasa ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa. Mutane sama da 400 sun mutu yayin da gidaje 12,000 suka lalace. Sannan matsalar ta tilasta wa mutane 40,000 barin gidajensu. Wani bincike ya nuna cewa sauyin yanayi ya sa yawan ruwan sama ya ninka sau biyu a Afirka ta Kudu, kuma karfinsa ya karu da kashi 8%.
Fari mai tsawo a gabashin Afirka
Yankin gabashin Afirka na fama da daya daga cikin fari mafi muni a shekarun baya-baya nan. An fara shi ne a shekarar da ta gabata kuma har yanzu yana ci gaba da gudana sakamakon karancin ruwan sama. Kimanin mutane miliyan 20 na fuskantar barazanar 'yunwa mai tsanani. Masana kimiyya sun ce rashin damana mai kyau da ke da nasaba da dumi na tekun Indiya, ya sa ana samun matsalar saukan ruwan sama.
Ambaliyar ruwa a Sydney
A farkon watan Yuli ne aka yi ambaliya ta hudu a cikin watanni 18 a Jihar New South Wales ta Ostareliya, musamman a Sydney. An yi kwatankwacin ruwan sama na watanni takwas a cikin kwanaki hudu kacal. Hanyoyi sun zama tamkar koguna, kuma an kwashe dubban mutane daga gidajensu. Firaminista Anthony Albanese ya ce ambaliyar ruwan ta tabbatar da bukatar daukar matakai kan sauyin yanayi.
Karancin ruwa a Italiya
Bayan karancin ruwan sama a damana da kuma fari na watanni, gwamnatin Italiya ta ayyana dokar ta baci a yankuna biyar na kasar. Dokar za ta ci gaba da aiki har zuwa karshen shekara. Birane da gundumomi sun sanya dokar takaita amfani da ruwa. Wannan dai shi ne matsalar ruwa mafi muni a tsawon shekaru 70 a yankin Po-Basin na kasar, wanda ke da muhimmanci ga noma da kiwo a Italiya.
Gobarar daji a Arewacin Amirka
Tun kafin a shiga lokacin da wutar daji ke addabar Amirka, wasu sassan kasar suka yi fama da wannan iftila'i. Wata gobara ta tashi a arewacin California a farkon watan Yuli, kuma habaka da ta yi a cikin dare ya tilasta wa daruruwan mutane kaurace wa matsugunansu. Wannan daya ne daga cikin gobarar da ta tashi a jihar, wacce kashi 96% ke fama da fari, a cewar hukumar sa ido kan fari ta Amirka.
Tsananin zafi a kasar Chaina
Chaina na fama da matsanancin zafi a cikin watannin Yuni da Yuli da ya zarta na shekaru da dama. Bukatar iskar air-condition ya sa yawan amfani da wutar lantarki a lardin Henan da ke gabashin kasar ya karu sosai. A halin da ake ciki, an yi ruwan sama a kudancin kasar. Gwamnati ta dora alhakin matsalar a kan sauyin yanayi, wanda ta ce zai kara yin tasiri ga al’umma da kuma tattalin arziki.
Zabtarewar kasa a kasar Brazil
Zabtarewar kasa da ambaliya biyo bayan mamakon ruwan sama sun yi awon gaba da gidaje a Jihar Pernambuco da ke Arewa maso gabashin Brazil a watan Mayu, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 100. Gidajen marasa galihu da aka gina a kan tsaunuka na fuskantar irin wannan bala'i kuma masana sun ce sauyin yanayi na taimakawa wajen kara yawan ruwan sama.