1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ilwad Elman: Gwarzuwa daga Somaliya

October 27, 2020

An zabi matashiya 'yar Somaliya a matsayin wadda ta samu lambar yabo ta Jamsu ga 'yan Afirka a shekara ta 2020. Mai shekaru 29 a duniya, ta na taimakon yaran da aka saka aikin soja da wadanda suka tsira daga fyade

https://p.dw.com/p/3kUt0
Somalia Mogadischu Ilwad Elman
'Yar fafutuka Ilwad Elman da ta lashe kyautar Jamus ga 'yan Afirka ta banaHoto: DW/A. Kriesch

A wannan Talatar ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ke mika wannan lambar yabo ga Ilwad Elman da take amfani da tsarin motsa jiki na Yoga, ga wadanda take taimako bayan sun shiga mawuyacin hali a kasar ta Somaliya da ta kwashe shekaru cikin rikici. Elman na taimakon yaran da aka tilasta musu shiga rikicin da mata da aka ci zarafinsu sake samun sabuwar rayuwa  a cibiyar da take aiki.

Mata 'yan Somaliya da suka koma gida

Shekaru 10 da suka gabata, matashiyar ta dauki hankali yayin da ta koma daga kasar Kanada inda take gudun hijira tare da mahaifiyarta, tana da shekaru 19 a duniya. Ilwad Elman ta ce tara kudin da za ta fara wannan aiki, ta kuma kara da cewa: "Mun fara cibiyar kula da wadanda suka fuskanci fyade saboda take hakkin dan Adam da mata da yara suka samu kansu a ciki. Mun saka yara da matasa wadanda kungiyoyin 'yan ta'adda suka dauka, wannan abu ne da yake da nasaba kai tsaye da 'yancin rayuwa da samun tsaro."

Ita kanta an halaka mahaifinta a shekarar 1996, kuma kusan shekara guda bayan haka an halaka yayarta. Hakan ya karfafa mata gwiwarta wajen aikin da take yi tare da yin tambayoyi.

Somalia Mogadischu Ilwad Elman bei der Beerdigung ihrer Schwester Almaas Elman
Ilwad Elman yayin jana'izar yayarta Almaas Elman da aka harbe har lahira a MogadishuHoto: Farah Abdi Warsameh/AP Photo/picture-alliance

Matashiyar da shaidawa Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yanayin da kasarta ta samu kanta. Wani abu da ke taimakon aikin da Elman ke yi, na zaman kafofin sada zumunta na zamani, kamar yadda take cewa: "Muna da hanyoyin sadarwa. Kowa na kan intanet. Matasa suna ba da labarin halin da suke ciki, ina alfaharin kasancewa cikin wannan bangaren da samar da dama, matasa sun dauki makomarsu wajen ba da labarinsu."

Yanzu ana kara samun labarin abin da ke faruwa. Ga Elman yana da muhimmanci a nuna wani yanayin dabam da ake da shi a Somaliya, ba wai rikici da yaki kadai ba. A shekaru 10 da suka gabata, Elman ta mayar da hankali kan ba da taimakon gaggawa a Somaliya amma yanzu ta ce lamura na sauyawa: "Aikinmu na sauya wa, daga bayar da taimakon gaggawa ga mutanen da suka shiga mawuyacin hali ko aka ci zarafinsu ko suka kadu, zuwa na kare abin da yake faruwa ta hanyar sauya al'adu ko aiki tare da gwamnati domin samar da dokoki."

Ita dai Ilwad Elman burinta shi ne sauya al'ummar Somaliya zuwa masu tabbatar da kare 'yanci da walwala. Kuma ta yi imanin matasa na tare da ita.