Turkiyya: Adawa ta karbi ikon birnin Istanbul
June 24, 2019Dama dai dan takarar adawar Imamoglu shi ne ya lashe zaben farko na ranar 31 ga watan Maris wanda hukumar zaben kasar ta soke a bisa dalillan samun kurakurai a cikin zaben. Kayin da dan takarar adawa kana na hannun damar Shugaba Recepp Tayyip Erdogan ya sha a wanann zabe na birnin Istanbul na zama wani babban komabaya ga jam'iyyar mai mulki ta AKP da aka jima ana yi wa kallon wacce ba ta kaduwa a fagyen zabe a kasar ta Turkiyya, sannan wata babbar barazana ce ga makomar mulkin Shugaba Erdogan a shekaru masu zuwa.
Dan takararta Ekram Imamoglu ya samu kashi 53 cikin 100 na kuri'un da aka kada yayin da tsohon firaminista kana dan takarar jam'iyyar AKP mai mulki Binali Yildrim ya samu kashi 45 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben magajin garin na birnin Istanbul na wannan karo. Bayan bayyana samakaon zaben, Imamoglu sabon magajin garin birnin na Istanbul ya bayyana gamsuwarsa da nasarar da ya samu tare da jinjina wa al'ummar kasar da ma gwamnati a kokarinsu na kare demokradiyya.
Tuni da Mista Yildrim dan takarar jam'iyya mai mulki ya amince da shan kaye tare da taya abokin hamayyar tasa murnar lashe zaben. Shi ma dai shugaban Turkiyya din Racep Tayyib Erdogan ya taya sabon magajin garin murna. Sai dai wani abu da ke nuni da irin ci-gaban da aka fara samu a dangantakar 'yan siyasa na bangaren adawa da na masu mulki a aksar ta Turkiyya shi ne irin yadda a birnin na Istanbul jama'a suka yi ta shagulgullan murna da bayyana ra'ayoyinsu mabambanta a wuri daya ba tare da cin zarafin juna ba.
tsawon kwanaki 18 a matsayin magajin garin na Santambul.