Tattalin arzikiGhana
Ghana za ta samu bashi daga IMF
October 6, 2023Talla
Kafin alkalmin na dala miliyan 600 da Ghanar za ta karba, zaai samu ne da zarar hukumar gudanarwar asusun na IMF ta sahale. Wata sanarwa da asusun ya fitar, ta ce wajibi ne Ghana ta hanzarta kammala nazarin tsarin da za ta bi wajen biyan bashin da kuma yadda za ta kashe kudin kamar yadda suka fara tattaunawa a kai a cikin watan Mayun wannan shekara. A bara ne dai Ghana ta nemi agajin asusun na IMF don ceto ta daga matsanancin halin matsin tattalin arzikin da ta shiga, wanda ke zaman mafi muni cikin tsawon shekaru.